Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya dakatar da ɗaya daga cikin manyan mataimakansa kan harkokin majalisa, King Indara, bisa zargin wallafa saƙonni a kafafen sada zumunta da aka ce suna ɗauke da kalaman rashin girmamawa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
An bayyana matakin ne cikin wata sanarwa da babban mataimakin Barau kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Shitu Madaki Kunchi, ya fitar a madadin Sanatan ranar Juma’a.

Kunchi ya ce matakin ya biyo bayan wasu rubuce-rubuce da sakonnin da aka danganta da Indara a kafafen sada zumunta, ciki har da wani saƙo mai taken “Abba Must Go” wato “Abba sai ya tafi.”
Ya ce an ɗauki waɗannan rubuce-rubuce a matsayin kalaman da suka nuna rashin girmamawa da rashin da’a ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sanarwar ta ce abin da Indara ya aikata ya saɓa wa ƙa’idojin jam’iyyar APC, musamman umarnin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan na goyon bayan jam’iyyar da kuma kare muradunta daga sama har kasa .
“Irin wannan ɗabi’a ta saɓa wa ƙa’idoji da tarbiyyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, da kuma manufofin jam’iyyar APC, musamman umarninsa na tallafawa da kare jam’iyyar daga sama har kasa.”
Read also: Gwamnatin Kano ta cika alkawarin biyan kuɗin makarantar daliban BUK
Read also: Labarin Wani Direban Tasi a Ingila da ke Karbar Albashin Aikin Gwamnati a Nigeria

Kunchi ya bayyana cewa an kawo ƙarshen nadin King Indara a matsayin Babban Mataimakin Harkokin Majalisa (SLA) a ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, daga ranar 18 ga Satumba, 2026.
Kano Times