Daga Rukayya Abdullahi Maida
Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Tarauni Hon. Hafizu Kawu ya kaddamar da aikin titu wanda za’a kashe kimanin naira biliyan 2.6 a karamar hukumar da yake wakilta.
Kadaura24 ta rawaito Titin mai tsawon kimanin kilomita 3 wanda ya hada titin Court Road, Karkasara, Darmanawa da kuma karshen Naibawa Yankatako ta hanyar Zariya, ya shafe shekaru da dama a lalace Kuma al’umma yankin sun jima suna kokawa a kan hakan rashin kyan titin .

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da aikin, wanda aka gudanar a ranar Laraba a titin Court Road, Hafizu Kawu ya ce wannan rana ce mai cike da tarihi a gare shi da al’ummar da suke amfani da titin saboda kaddamar da aikin.

Dan majalisar ya ce aikin yana da mahimmanci kuma zai taimaka wajen inganta zamantakewa da tattalin arzikin al’ummar yankin da karamar hukumar baki daya.
A cewarsa, hanyar ta jima tana damun al’ummar karamar hukumar Tarauni, Amma wannan aikin zai kawo karshen wahalhalun da al’ummar suka dade suna fuskanta sakamakon fara aikin sake gina hanyar.
“Hanyar hanya ce da ta hada Tarauni da sauran kananan hukumomi da ma wasu manyan tituna da mutane ke bi domin zuwa wasu jihohin.” Inji Hafizu Kawu
Ya kuma bayar da tabbacin kammala aikin cikin gaggawa, dan majalisar ya yi kira ga al’ummar mazabar da su baiwa ma’aikatan cikakken hadin kai a yayin gudanar da aikin.
Ya kuma yi kira ga dan kwangilar da ya tabbatar an yi aiki mai inganci .
A nasa jawabin, mai kula da ayyukin, Engr. Ibrahim, ya ce dan majalisar na Tarauni shi ne ya jagoranci samo aikin daga ma’aikatar ayyuka ta kasa.
Ya ce an ba shi aikin kula da aikin, inda ya tabbatar da cewa zai tabbatar da an yi aiki mai inganci Kuma cikin gaggawa.