Shugaban Gidan Rediyon Nigeria, Pyramid FM Kano, Dr. Garba Ubale, ya yabawa Darakta-Janar na Tinubu Support Groups (TSG) na Arewa maso Yamma, Dr. Baffa Babba Dan’agundi, bisa daukar nauyin gyaran motar gidan rediyon da aka lalata yayin harin da wasu ’yan daba suka kai wa ma’aikatan gidan a wajen taron jam’iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan daba sun kai wa motar Pyramid FM hari ne yayin da ma’aikatan ke kan hanyarsu ta komawa ofishinsu bayan kammala daukar rahoton taron kai tsaye, inda aka lalata motar kafin daga bisani lamarin ya jawo Allah-wadai daga kungiyoyin ’yan jarida.

Da yake yabawa Dr. Baffa Babba Dan’agundi kan wannan mataki, Dr. Garba Ubale ya bayyana abun da yayi a matsayin kishin al’umma da kuma nuna sanin muhimmancin kafafen yada labarai wajen gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu.
Ya ce daukar nauyin gyaran motar ya zo ne a daidai lokacin da ake bukata, musamman ganin cewa motar na daga cikin kayan aikin da ma’aikatan Pyramid FM ke amfani da su wajen kai wa jama’a sahihan labarai daga wurare daban-daban.
Dr. Ubale ya kara da cewa irin wannan hali na taimakon kafafen yada labarai da ma’aikatansu ya kamata ya zama abin koyi ga sauran masu ruwa da tsaki, musamman ‘yan siyasa.
A cewar sa, aikin jarida ba na wata jam’iyya ko wani dan siyasa ba ne, illa dai wata muhimmiyar hanya ce ta isar da bayanai ga al’umma da kuma karfafa dimokuradiyya.
Shugaban Pyramid FM ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani nau’in tashin hankali ko barazana ga ’yan jarida yayin gudanar da ayyukansu.
Ya ce dole ne a samar da yanayin da zai bai wa ’yan jarida damar gudanar da aikinsu cikin ’yanci da tsaro, ba tare da fargabar kai musu hari ko lalata kayayyakin aikinsu ba.
Harin dai ya jawo Allah-wadai daga Kungiyar ’Yan Jaridu ta Kasa (NUJ), reshen Kano, wadda ta ce kai hari ga ’yan jarida da lalata motar Pyramid FM barazana ce ga ’yancin aikin jarida da kuma ci gaban dimokuradiyya.
NUJ ta kuma yi kira da a gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka kai harin tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a lamarin a gaban kotu.

A nasa bangaren, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kuma bayyana harin a matsayin abin takaici, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su binciki lamarin.
Daukar nauyin gyaran motar da Dr. Baffa Babba Dan’agundi ya yi na kara jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki wajen kare martabar aikin jarida da tabbatar da zaman lafiya a lokacin siyasa.