Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan tawagar ’yan jarida da suka halarci taron kaddamar da shugabannin gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Rahotanni sun cewa lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala taron, wasu ’yan daba sun far wa motar da tawagar ’yan jaridar ke ciki, inda suka farfasa gilasan motar tare da lalata wasu sassan motar ta amfani da adda da wukake da kokara.

Kadaura24 ta rawaito Ma’aikatan Pyramid da lamarin ya shafa sun hadar da Yakubu Abubakar Gwagwarwa da Shafi’u Abdullahi Panshekara da Ibrahim Hussaini da kuma Abdulmajid Habib Tukuntawa .

Sauran Wadanda suke Mota akwai wasu jami’an ƴansanda da ma’aikacin Guarantee Radio Abdulbaki Ali Ahmad Shariffai.
Sai dai Har yanzu babu cikakken bayani kan ko an kama wadanda ake zargi da hannu a lamarin na farma Tawagar Yan Jaridar