‎Sheikh Sammani Makwarari Ya Bukaci Gwamnatin Kano Ta Dauki Mataki Kan Rahoton Majalisar Shura

Date:

Daga: Kamal Yakubu Ali

‎Wani malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Dr. Sammani Bunyamin Makwarari, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta karɓi rahoton da Majalisar Shura ta gabatar mata dangane da batun Sheikh Lawan Abubakar Triumph, tare da ɗaukar matakin da ya dace domin tabbatar da adalci da kare martabar Manzon Allah ﷺ.

‎Sheikh Sammani ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke gabatar da Hudubar Juma’a a Masallacin Juma’a na Muhammad Dangote da ke unguwar Alfindiki, a ƙaramar hukumar Birnin Kano.

IMG 20260704 WA0007
Talla


‎Malamin ya ce al’ummar jihar Kano na jiran ganin matakin da gwamnatin jihar za ta ɗauka kan mutanen da suke furta kalamai ko yin abubuwan da suka shafi martabar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad ﷺ.

‎Ya bayyana cewa babban abin da al’ummar Kano ke buƙata shi ne a yi aiki da abin da rahoton Majalisar Shura ya ƙunsa, ta hanyar miƙa shi ga hukumomin da ke da alhakin shari’a, musamman kotu, domin ta tantance zargin da ake yi.

‎Bai wa ƙananan hukumomi cikakken ’yanci zai taimaka wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a Najeriya – Mukhtar Gora

‎Sheikh Sammani ya ce idan kotu ta tabbatar da cewa wanda ake zargi ya aikata laifi, to ya kamata a ɗauki matakin da doka ta tanada a kansa.

‎Ya ƙara da cewa Kano gari ne da aka san shi da ƙaunar Manzon Allah ﷺ, don haka wajibi ne hukumomin jihar su tabbatar da cewa ana kare martabarsa tare da kiyaye zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

IMG 20260704 WA0005
Talla


‎A cewarsa, ɗaukar matakin da ya dace zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano, tare da ƙarfafa amincewar al’umma ga hukumomin gwamnati.

‎Ya kuma buƙaci gwamnatin jihar da ta yi abin da ya dace wajen kare martabar Manzon Allah ﷺ, yana mai cewa hakan na daga cikin matakan da za su taimakai maka wajen tabbatar da zaman lafiya .

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Bai wa ƙananan hukumomi cikakken ’yanci zai taimaka wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a Najeriya – Mukhtar Gora

‎Daraktan Janar na Ƙungiyar Mataimakan Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta...

‎An Mayar Da Mu Kamar Barayi”: Masu Downloading a Kano Sun Zargi Hukumar Tace Fina-finai Da Muzguna Musu

‎Guda cikin masu sana’ar tura fina-finai, wato Downloading, Abdulsam...

‎Ku daina rabon tallafin babura — Ministan Tsaro ga gwamnoni

‎ ‎Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya ce...

Ganin El-Rufa’i ya jawo ICPC ta kori jami’inta

Hukumar ICPC ta kori wani jami’inta mai suna Daniel...