Daraktan Janar na Ƙungiyar Mataimakan Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGOVC), Hon. Muktar Dahiru Gora, ya ce bai wa ƙananan hukumomi cikakken ’yancin cin gashin kansu da kuma damar sarrafa kuɗaɗensu kai tsaye, na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu sassan ƙasar.
Gora ya bayyana cewa ƙananan hukumomi su ne matakin gwamnati mafi kusa da al’umma, don haka suna da cikakkiyar masaniya kan matsalolin da jama’a ke fuskanta, musamman matsalolin tsaro, talauci da rashin ayyukan yi.

Ya ce idan aka bai wa ƙananan hukumomi damar amfani da kuɗaɗen da ake ware musu kai tsaye, za su iya aiwatar da shirye-shiryen raya karkara, samar da ayyukan yi da tallafawa matasa, lamarin da zai rage yawan mutanen da ke shiga harkar ta’addanci da sauran miyagun ayyuka.
Daraktan Janar ɗin ya yi nuni da kalaman Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), wanda ya jaddada cewa ƙananan hukumomi da al’ummomin yankunan ƙasar suna da muhimmiyar rawa wajen samar da ingantaccen tsaro, saboda su ne suka fi sanin yanayin yankunansu da matsalolin da ke addabar al’ummominsu.
A cewarsa, rashin cikakken iko da albarkatun kuɗi a matakin ƙananan hukumomi na iya kawo cikas ga ayyukan ci gaba da kuma matakan da ake ɗauka wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ganin El-Rufa’i ya jawo ICPC ta kori jami’inta
Gora ya kuma yi kira ga gwamnoni da su tabbatar da cewa ƙananan hukumomi suna samun kuɗaɗen da aka ware musu kai tsaye, domin su samu damar gudanar da ayyukan da suka shafi rayuwar jama’a ba tare da dogaro da wasu matakai ba.
Ya ce yin hakan zai taimaka wajen rage talauci, bunƙasa tattalin arzikin karkara da samar da damarmaki ga matasa, wanda a ƙarshe zai taimaka wajen rage abubuwan da ke haddasa rashin tsaro.
“Idan ƙananan hukumomi suka samu cikakken ’yanci da kuɗaɗensu, za su fi samun damar sanin matsalolin jama’arsu tare da magance su cikin gaggawa,” in ji shi.
Gora ya ƙara da cewa tsaro ba ya ta’allaka ne kawai ga jami’an tsaro, domin akwai buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da al’ummomi.
Ya ce ƙarfafa ƙananan hukumomi zai ba su damar taka rawar da ta dace wajen samar da ayyukan more rayuwa da kuma tallafa wa tsarin tsaro daga tushe.

Idan za a iya tunawa dai A shekarar 2024, Kotun Ƙoli ta Najeriya ta tabbatar da ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi, ciki har da batun samun rabonsu na kuɗaɗen tarayya kai tsaye, matakin da masu rajin ƙarfafa ƙananan hukumomi ke ganin zai taimaka wajen inganta shugabanci a matakin ƙasa.
Gora ya ce lokaci ya yi da za a mayar da hankali wajen ƙarfafa ƙananan hukumomi domin su zama ginshiƙin samar da tsaro, ci gaban tattalin arziki da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar Najeriya.