Matsalar tsaro: Gwamnan Kano Abba ya ziyarci Tsanyawa da Shanono

Date:

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya ziyarci sansanin rundunar haɗin gwiwa ta JTF a Karamar Hukumar Tsanyawa, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro wajen magance barazanar tsaro da ta taso a yankin.

Gwamnan ya ce ziyarar tasa ta nufin tantance halin tsaro da ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro, yana mai bayyana cewa ayyukan JTF za su dawo da zaman lafiya a yankunan da suka gamu da hare-hare.

InShot 20250309 102512486

Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ba da dukkan goyon baya, musamman a fannin jin daɗin jami’an tsaro da samar da kayan aiki, tare da tabbatar da cewa waɗanda aka sace za a kubutar da su cikin koshin lafiya.

Gwamnatin Kano ta bayyana kananan hukumomin da ta haramta Achaba

Shugaban rundunar ta 3 na Sojan Najeriya, Birgediya Janar Ahmed Tukur, ya bayyana cewa rundunar ta ƙunshi jami’an soji, rundunar sojan sama, ‘yansanda, DSS, NSCDC da ‘yan sa-kai, kuma suna gudanar da ayyuka a wuraren da ake fama da barazana.

Gwamnan ya kuma ziyarci kauyen Yankamaye, inda aka sace mutane shida tare da kashe wata tsohuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...