Da dumi-dumi: Tinubu ya aikawa majalisa sunan wanda zai nada Ministan Tsaro

Date:

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sunan Janar Christopher Gwabin Musa ga majalisar dattawa domin tabbatar da shi a matsayin sabon Ministan Tsaro.

Wannan na zuwa ne bayan murabus din da tsohon ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi a ranar Litinin.

Rundunar ’Yan Sandan Kano ta fitar da sabbin dokoki ga masu babura da adaidaita sahu

Janar Musa, wanda ya taba jagorantar rundunar tsaro ta ƙasa daga 2023 zuwa Oktoba 2025, ya kasance gogaggen jami’in soja mai shekaru 58, kuma ya taba samun lambar yabo ta Colin Powell a 2012. An haife shi a Sokoto, inda ya yi karatunsa na firamare da na sakandare kafin ya shiga makarantar horar da sojoji ta NDA a 1986.

FB IMG 1764684972412
Janar Christopher Musa

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanyawa Hannah.

InShot 20250309 102512486

A tsawon aikinsa, ya rike muhimman mukamai a rundunar sojin Najeriya, ciki har da zama kwamandan Sector 3 a hare-haren yaki da ta’addanci, da kuma jagorantar Operation Hadin Kai kafin daga baya ya zama Hafsan Tsaro a 2023.

A wasikar da ya aika wa majalisar dattawa, Shugaba Tinubu ya ce yana da cikakken tabbaci cewa Janar Musa zai karfafa tsarin tsaron ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...