An gudanar da wani gagarumin taron karɓar Hon. Sule Musa Kadawa, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ungoggo, tare da dimbin magoya bayan jam’iyyar NNPP/ Kwankwasiyya da suka sauya sheƙa zuwa APC a ƙarƙashin tafiyar A.A Zaura.
Hon. Kadawa ya shiga jam’iyyar APC ne tare da magoya baya sama da 2,000, inda suka bar jam’iyyarsu gaba ɗaya domin shiga tafiyar A.A Zaura, wadda ya bayyana a matsayin tafiyar ceton al’umma.

Da yake jawabi, Sule Musa Kadawa ya ce abin da ya ja hankalinsa zuwa tafiyar A.A Zaura shi ne nagartar halayen Zaura da kuma yadda yake zuba jari wajen taimakon jama’a ba tare da nuna bambanci ba.
Ya ce matakin da suka ɗauka tamkar buɗe sabon shafi ne a siyasar karamar hukumar Ungoggo da Kano baki ɗaya.
Hon. Kadawa ya kuma nanata shirye-shiryensu na haɗa kai da dukkan magoya bayan APC na ƙaramar hukumar Ungoggo da ma jihar Kano domin ƙarfafa jam’iyyar APC da tabbatar da ci gaban al’umma.
Matasan dake harkar daba suna da baiwar da zata ciyar da kano gaba- Waiya
A yayin taron, da daruruwan jama’a suka halarta jagororin APC sun yi wa sabbin wadanda suka shiga jam’iyyar maraba tare da bayyana cewa wannan sauyi zai ƙara wa jam’iyyar kuzari a yankin.