Ministan Kimiyya da Fasaha na Najeriya, Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa.
Hakan ma kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar.
Rahotanni sun bayyana cewa ministan ya tsinci kansa cikin ce-ce-ku-ce ne tun bayan wani binciken jaridar Premium Times da ya gano cewa takardar shaidar karatun sa (degree) da takardarsa ta bautar Kasa NYSC na jabu ne.
Shugaban jami’ar Nsukka (UNN), Farfesa Simon U. Ortuanya, ya bayyana wa Premium Times cewa duk da cewa Nnaji ya fara karatu a jami’ar a shekarar 1981, bai kammala karatunsa ba, kuma jami’ar bata taɓa ba shi shaidar kammala digiri ba.
Sai dai sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar ta ce Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya karbi murabus din nasa.