Tinubu ya bukaci Majalisa ta amince ya ciyo bashin dala biliyan $2.35

Date:

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wa majalisar wakilai yana neman amincewarta domin ciyo bashin dala biliyan $2.347 daga kasuwar kuɗin ƙasashen waje domin cike gibin kasafin kuɗin 2025 da kuma sake biyan tsohon bashin Eurobond da zai ƙare a watan Nuwamba 2025.

Haka kuma, Shugaban ƙasar yana neman amincewar majalisar wajen fitar da tsarin bashi mara Ruwa na Sukuk na farko a duniya, wanda darajarsa ta kai dala miliyan $500, domin aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa.

Tinubu ya ce buƙatar tana da tushe bisa ga tanade-tanaden Dokar Hukumar Gudanar da Bashi ta Ƙasa ta 2003, tare da nufin ƙarfafa damar Najeriya wajen samun kuɗaɗen kasashen waje da kuma gujewa jinkirin biyan bashi.

Ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen ɗaukar bashin, ciki har da Eurobond, bashin haɗin gwiwa, ko lamunin kai tsaye daga cibiyoyin kuɗi na duniya.

A cewar Tinubu, tsarin Sukuk ɗin da ake shirin fitarwa zai taimaka wajen gina ababen more rayuwa da kuma haɓaka kasuwar takardun gwamnati kamar yadda aka yi da Sukuk na cikin gida tun daga shekarar 2017.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...