Ra’ayi: Kabir Abubakar Bichi, na iya zama raba gardamar yan takarar gwamnan Kano 2027 a APC

Date:

Ra’ayin Bashari Habib Tarauni

Na dade ina bibiyar siyasar Kano, kuma abu ɗaya da na sani shi ne: babu zaɓen da ke zuwa da sauƙi a wannan jiha. Kano jiha ce mai nauyi a siyasar Najeriya, kuma duk jam’iyyar da ta yi nasara a nan, tana iya yin tasiri a matakin Kasa baki daya.

Jihar kano jigo ce a wajen jam’iyyar APC. Amma yayin da 2027 ke kara matsowa kusa, ina da damuwa matuƙa. Ba wai don jam’iyyar ba ta da shugabanni masu ƙarfi ba, sai don barazanar rikicin da zai iya ballewa tsakanin magoya bayan Sanata Barau Jibrin da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, lamarin da ka iya jefa jam’iyyar cikin hali mai wuya.

FB IMG 1753738820016
Talla

Gaskiyar magana, Sanata Barau da Dr. Gawuna dukkansu ‘yan siyasa ne da nake girmamawa ƙwarai. Barau ya ɗaga darajar Kano a matakin ƙasa da matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa, yana amfani da ofishinsa wajen kare muradun jihar. Yayin da shi kuma Gawuna ya tabbatarwa da duniya cewa shi Dan jam’iyya ne mai biyayya kuma jigo tun daga lokacin da ya yi jam’iyyar takarar gwamnan jihar Kano aa zaben da ya gabata. Dukkaninsu jigo ne a jam’iyyar APCn Kano .

Nasarorin mutum ba su kadai ake bukatar a Siyasa ba Ita Siyasa ba, tana bukatar hadin kan sauran abokan tafiya da haɗin kan magoya baya. Yanzu haka, gaba tsakanin magoya bayan wadannan jagorori biyu na ƙara zafi, abin da zai iya haifarwa da jam’iyyar matsala a zaben 2027 kuma zai yi wuya a iya magance matsalolin nan kusa. Idan hakan ta faru, jam’iyyun adawa za su samu dama.

Saboda haka nake ganin lokaci ya yi da jam’iyyar za ta duba wani Wanda zata Sanya a gaba Wanda zai iya haɗa kawunan ɓangarorin biyu. A ganina, Injiniya Kabir Abubakar Bichi, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bichi kuma shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai ne kadai zai iya wannan aikin.

Eh, gaskiya ne, Kabir Bichi bai nuna sha’awa ga wannan tserin ba. Amma wannan ma shi ne dalilin da ya sa nake ganin ya dace. Bai taɓa bari a jawo shi cikin rikice-rikicen siyasa ba, sai dai ya maida hankali wajen aikinsa a majalisa da hidimar al’ummarsa. Ba shi da son mulki, kuma hakan ya sa ya dace APC ta lallashe shi ya karbi Wannan tsarin.

A zahiri, mazabar Bichi ta sami ci gaba mai ban mamaki a ƙarƙashinsa. Akwai hanyoyi da aka yi wa kwalta, wutar lantarki da aka kai ƙauyuka, da ayyukan samar da ruwan sha da suka inganta rayuwar al’ummar bichi. Ya kuma zuba jari sosai a fannin ilimi ta hanyar bayar da guraben karatu ga ɗalibai da dama a gida da ƙasashen waje. Haka kuma, ya kaddamar da aikin wutar lantarki Mai amfani da hasken rana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, wanda ya dukkanin al’ummar jihar kano za su amfana .

Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Aikin samar da wutar sola na Naira Biliyan 12 a asibitin Malam Aminu Kano

Haka kuma, ayyukan jinƙansa sun zarce iyakacin mazabarsa. Mutane daga sassa daban-daban na Kano na iya ba da shaida kan irin taimakon da ya yi musu kai tsaye ko kuma ta wata hanyar. Irin wannan jagoran jam’iyyar APC ke bukata a yanzu — mai haɗa kai, ba mai rarraba kan jama’a ba.

Ba wai ina nufin a yi watsi da Sanata Barau ko Dr. Gawuna ba. A’a, gudummawar da suka bayar ta fi a misalta, Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, a samu haɗin kai da daidaito fiye da fifita burin mutum guda.

Kano tana da girma da muhimmancin da ta fi karfin a yi wasa da ita a Siyasa musamman a zaben 2027 . Don haka nake ganin Idan aka lallashe Kabir Bichi ya fito a matsayin wanda aka hada kai aka zaɓo, jam’iyya za ta yi kwargini da daraja har a idon yan adawa.

 

A ganina, lokaci ya yi da jam’iyya za ta matsa masa ya taka rawa mafi girma ko da bai nema ba, wani lokaci jagorancin akan zabo shugaban ko da shi ba ya so ya shugabanci al’umma, Idan abin da APC ke buƙata domin ta ci Kano a 2027 shi ne haɗin kai, to Kabir Abubakar Bichi shi ne mafi dacewa.

Wannan ra’ayina ne na gaskiya, wanda ya samo asali daga ƙaunata ga jam’iyyata da jihata. APC ba za ta iya shiga 2027 da rarrabuwar kawuna ba. Muna bukatar wanda zai iya hade kan al’umma kuma wanda zai kaimu ga yin nasara, kuma a ganina wannan mutum shi ne Kabir Abubakar Bichi.

Daga  Bashari Habib Tarauni (bashirhab@gmail.com)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Al’ummar Tokarawa, Gorubai, Garawa da Yarawa sun koka kan matsalar hanya da rashin gada

Al’ummar garuruwan Tokarawa, Gorubai, Garawa, Yarawa da Dan Tsuku...

Kungiyar ODPMNigeria ta shirya taron tattaunawa da matasa a Bichi

Daga Ahmad Isa Getso   Ƙungiyar Rajin Kawo Sauyi da Cigaba...

Yadda Dansanda ya harbe kansa da bindiga a Kano

Wani jami’in dansanda mai suna Aminu Ibrahim ya rasa...

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...