Amfani da al’ada a cikin fina-finan kannywood ne ya hana masa’antar ci gaba – Khadija Osi

Date:

Jaruma a masana’antar Kannywood Khadija Muhammad wacce aka fi Sani da Khadija Osi ta bayyana cewa amfani da aka da al’ada a fina-finan masana’antar ne ya hanata yin gogayya da takwarorinta na Duniya .

Khadija Osi ta bayyana hakan ne cikin Shirin “Daga Bakin Mai ita” na tashar BBC Hausa Wanda suke Gabatarwa a kafafen sada zumunta .

Jarimar ta ce da ace Kannywood za su daina Sanya al’ada a cikin fina-finansu tabbas da cikin kankanin lokaci masana’antar za ta yi kafa da kafa da takwarorinta na Duniya .

” Harkar Entertainment harka ce nishadantarwa ba wai harkace da za a rika dauko al’ada ana sanyawa a ciki ba, duk fina-finan Duniya ba sa Sanya al’ada a cikin fina-finansu , sai dai idan labari ne ya zo da hakan, inda za mu rika yin fina-finanmu na Hausa kamar yadda suke yi mu ma da tuni mai kai inda suka kai”. Inji Khadija

“Na taɓa yin aure a baya har ina da yaro ɗaya, amma yanzu ba ni da aure cewar Khadija Osi

FB IMG 1753738820016
Talla

Jarumar wadda ta ke ƴar jihar Borno ta bayyana yadda ta samu kanta a masana’antar fina finan Hausa inda tace.

” An haife ni a Maiduguri Babana shuwane, mahafiyata bafullatana na girma a Maiduguri nayi karatuna acan har na shigi Kannywood.

Nasarar da Ɗaliban Kano suka Samu a NECO Kokari ne na Gwamnatin Ganduje – Sanusi Kiru

Da farko mahafina bai yadda ba duk da naso harkar fim tun ina yarinya saboda inda rawar kai, da son harkar nishaɗantarwa Shiyasa naso fim har Allah yasa nazo ta hannun Marigayi Nura Mustapha Waye. Inji Osi.

Abinda ke ɓatan rai a rayuwa shi ne na ga anci amana ba na so na ga wani ya ci amanar wani, bani da babbar ƙawa a fim, sai dai kuma babban abinda ke sani farin ciki shi ne na yi Salatin manzon Allah da kuma ganin mahaifiyata.

Abin da ba zan manta dashi a rayuwata ba bai wuce rasuwar mahaifina ba Cewar Khadija Osi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...