Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Aikin samar da wutar sola na Naira Biliyan 12 a asibitin Malam Aminu Kano

Date:

Kwana biyu bayan rikicin wutar lantarki tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin samar da megawatt bakwai (7MW) na wutar sola a asibitin.

Yayin bikin kaddamar da aikin a Kano a jiya Laraba, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Bichi, Abubakar Bichi, ya bayyana cewa an ware fiye da naira biliyan 12 domin aikin, wanda ake sa ran zai baiwa asibitin wutar lantarki ba tare da dogaro da tsarin wutar lantarki ta kasa ba.

Bichi, wanda shi ne ya kawo aikin, ya ce wannan shiri ne na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da sola ga dukkan manyan makarantu da asibitocin koyarwa a fadin kasar, inda aka fara da Asibitin Malam Aminu Kano AKTH.

Ya nuna godiya ga Shugaba Tinubu bisa amincewa da kuma goyon bayan wannan aiki.

FB IMG 1753738820016
Talla

A nasa jawabin, Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Uche Nnaji, ya ce wannan aiki farkon mataki ne na aiwatar da shirin Sabon Fata da gwamnatin Tinubu ta zo da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...