Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhinin sa kan rasuwar dattijo, fitaccen ɗan kasuwa kuma mai bayar da gudunmawar al’umma, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a safiyar Asabar, 28 ga Yuni, 2025.
A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Dantata a matsayin jarumin ƙasa da kuma babban rashi ga Najeriya, sakamakon gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar.

“Alhaji Dantata zai ci gaba da kasancewa cikin tarihin Najeriya saboda kwazonsa, jajircewarsa, da kishin ƙasa da ya nuna ta hanyar sana’o’in kasuwanci da ayyukan jin ƙai da suka shafi rayuwar dimbin ‘yan Najeriya,” in ji Shugaba Tinubu.
Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa
Marigayin ya shahara da basirarsa a harkar kasuwanci, kuma ya taka rawar gani a fagen hidimar jama’a, inda ya taba zama Kwamishinan Tsare-tsare da Ci Gaban Tattalin Arziki a tsohuwar Jihar Kano da sauran muhimman mukaman gwamnati.
Shugaba Tinubu ya kuma ambato irin alaƙar da ke tsakaninsa da marigayin, inda ya bayyana shawarwarin da ya ba shi da goyon bayan da ya nuna masa a matsayin abin karfafa gwiwa da amfani ƙwarai.

Haka kuma, shugaban ya yaba da ayyukan jin ƙai na Alhaji Dantata, musamman a fannonin ilimi da kula da lafiya, wadanda suka taimaka wa rayuwar mutane da dama a fadin ƙasa.
Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Dantata, Gwamnatin Kano da al’ummar jihar bisa wannan babban rashi, yana mai cewa Najeriya ta rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yanta.