Sallah: Ku sanya Kano da Nigeria a addu’o’iku na wannan lokacin – Kano ALGON ga jama’a

Date:

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo

Shugabar karamar hukumar Tudun Wada kuma Shugabar Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomin jihar kano (ALGON) Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u Soja ta taya daukacin Al’ummar musulmi murnar idin Sallah Babba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Shugabar ya fitar kuma ya aikowa Jaridar Kadaura24.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Hajiya Sa’adatu soja (ALGON) tace
“Amadadin al’ummar karamar hukumar Tudun wada da na kananan hukumomi (44) na Jihar Kano nake taya al’ummar Musulmin duniya musamman jihar Kano da karamar hukumar Tudunwada murnar bikin Babbar Sallah (Eid-el-Kabir) ta shekarar 10/12/1446 bayan hijjra, wacce tayi daidai da 06/06/2025.

Hon. Mustapha Buhari Bakwana ya aikewa yan APC da al’ummar Kano Sakon Barka da Sallah

Ta kara da cewa “Muna kara godiya ga Allah Subhanahu Wata’Alah da ya nuna mana wannan babbar rana mai daraja, Allah ka maimaita mana ya Allah ka gafarta mana kura-kuren mu, ka karbi kyawawan aiyukan mu.

“Ina yiwa Mai girma gwamnan Kano da mataimakinsa da Sarakunan Kano da Rano da Karaye da Gaya Barka da Sallah da fatan Allah ya maimaita mana ta bashi” . Inji ALGON

InShot 20250309 102403344

A karshe tayi fatan ‘yan uwa musulmai zasu cigaba da yiwa Kasa Najeriya da Jihar Kano da karamar hukumar su ta Tudunwada addu’a, Allah ya kawo zaman lafiya mai dorewa, tare da fatan samun yalwar arziki da dukiya mai albarka dafatan Allah ya bada damuna mai albarka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...