Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sunusi na biyu, ya hori al’ummar Musulmi da su hada kawunansu don ci gaban addinin Islama.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da ya gabatar da hudubar sallar Idi a babban masallacin Idi da ke Ƙofar Mata a Kano.

“Masu hali ku ƙara himma wajen taimakon masu ƙaramin ƙarfi dake cikin al’umma musaman a wannan lokaci na sallar Idin Layya, don neman yardar Allah maɗaukakin Sarki, in ji Sarkin”.
Sarki Sanusi na biyu, ya kuma miƙa saƙon barka da Sallah, ga al’ummar Musulmi, inda ya buƙaci jama’a da su yi amfani da wannan dama wajen sanar da soke haye hayen Sallah, da aka saba gudanarwa bisa ga sha’anin kalubalen tsaro.
Daganan Sarkin ya kuma yi kira ga iyaye da su ƙara ƙaimi wajen sanya idanu ga tarbiyar ƴaƴansu, don kare su daga shiga gurɓatattun halaye na Daba da ƙwacen Waya da sauran munanan ayyuka.