Babbar Kotun Shari’a da ke Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani mutum da ya kunna wuta a cikin wani masallaci, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane da kuma jikkatar da dama.
Lamarin ya faru ne a ranar 15 ga watan Mayu, 2024, a kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano.

Mai shari’a Halhatu Huza’i Zakariyya ne ya yanke hukuncin bayan ya samu wanda ake tuhuma da laifuka hudu da suka shafi kashe-kashe da haddasa munanan raunuka.
Kotun ta bayyana cewa laifin da aka aikata ya saba wa doka, kuma hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da laifin mutumin ba tare da tantama ba.