BUƊAƊƊIYYAR WASIƘA ZUWA GA MAIGIRMA SHUGABAN MA’AIKATAN GWAMNATIN JIHAR KANO ALHAJI ABDULLAHI MUSA
FITOWA TA FARKO:
Bayan gaisuwa da fatan ansha ruwa lafiya.
Na zaɓi wannan lokaci da kuma wannan kafa ne domin aikawa da saƙon karta kwana, duba da ɗinbin buƙatu da wannan yanki namu na Kano ta Kudu da kuma Kiru/Bebeji yake ciki.
Ya maigirma Shugaban Ma’aikata, inaso na tuna maka cewar wannan babbar kujera an baka ita ne domin kasancewar ka ɗan wannan yanki namu mai albarka na Kano ta Kudu inda ka fito daga garin Kwanar Ɗangora, ƙarƙashin Mazabar Kiru da Bebeji kuma domin ka yi amfani da ita kujerar wajen taimakon yankin. Amma har yanzun babu abunda kayi wa Kwanar Ɗangora garin ka, ko Ƙiru ƙaramar hukumar ka, ko kuma Ƙiru da Bebeji kwanstituwensin ka, balantana kuma Kano ta Kudu yankin daka fito. Mun san babban burin ka shine ka zama Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu amma tsakanin ka da Allah, a haka zaka cimma wannan burin naka?

Masu sauraro nasan zaku tuna cewar, kafin Shugaban ma’aikata ya ɗare wannan kujera, wacce a yanxu haka har Maigirma Gwamna ya ƙara masa wa’adi, sai da Shugaban ma’aikata ya shafe kimanin Shekaru 35 yana aikin Gwamnati har ya taka manya- manyan matsayi masu muhimmanci daban- daban har zuwa Babban Sakatare (wato, Permanent Secretary na fadar gwamnatin Kano), amma ni dai a iya sani na bansan ta yadda yayi amfani da wannan damar ya taimaki wannan yankin namu wanda ya fito ba. Misali:
Zai yi kyau mutane su tuna cewar kujerar Shugaban Ma’aikata tana cikin jerin manyan Kujeru guda 5 masu girma a faɗin Jihar Kano, ma’ana ya na cikin waɗanda ake kulle ƙofa da su domin yanke hukunci a Jihar baki ɗaya.
Abun lura a nan shi ne, wai jama’a za su iya tuna ko Shugaban ma’aikata yayi amfani da damar mulkinsa da kusancin da ke tsakaninsa da Mai girma Gwamna wajen samarwa mutanen yankin mu wanni tagomashi musamman akan fannoni daban-daban da suka shafi cigaban rayuwar jama’ar mu na Kano ta Kudu, Ƙiru da Bebeji ko kuma Ƙiru?
Tambayoyi na a nan sune:
1. Wai shin Maigirma Shugaban ma’aikata wane mataki ka ɗauka akan gyara tare da gina Sababbin Makarantu Manya da Ƙanana a Kiru, Kiru da Bebeji da Kano ta Kudu?
2. Wanne mataki ka ɗauka a kan gyara tare da gina sababbin manyan asibitocin mu, kama daga Asibitin Kiru, Yako, Kwanar Ɗangora, Bebeji, Tariwa, Tiga, Rano, Sumaila, Tudun Wada da makamantan su a Kano ta Kudu?
Bincike: Shin Sabon Hakimi ya shiga gidan sarautar Bichi kuwa ?
3. Wai shin maigirma Shugaban ma’aikata wane mataki ka ɗauka akan gyara tare da kawo Sababbin Boreholes, Kananan Dama-damai da jawo ruwan Dam ɗin Tiga zuwa Bebeji domin noman Rani da kuma Dam ɗin Challawa Goje zuwa Ƙiru da makamantan su a Kano ta kudu?
4. Wanne mataki ka ɗauka akan wasu daga cikin muhimman hanyoyin mu. Misali: hanyar da ta tashi daga Ƙiru zuwa Ba’awa; Kwanar Ɗangora zuwa Badafi; Ƙiru zuwa Fagoje zuwa Achilafiya; Ƙiru zuwa Alhazawa zuwa Ƙwanar Zuwo; Tashar Ɗantako zuwa Unguwar Turu zuwa Achilafiya; Ɗangora zuwa Ɗansoshiya; Bebeji zuwa Yako; Bebeji zuwa Madobi; Gwarmai zuwa Tiga/Anadariya; Dakatsalle zuwa Baguɗa zuwa Bebeji; Kasuwar Dogo zuwa Tariwa zuwa Bebeji da makamantan su a yankin ka da kuma makamantan du a Kano ta kudu?
5. Maigirma Shugaban ma’aikata, muna sane da cewa wannan kujerar da ka ke kai, kujera ce mai ƙarfin gaske. Wai shin wanne gagarumin taimako ka taɓa yiwa jama’ar wannan yankin namu, musamman wajen Taimakon Jama’a domin su rabauta da muƙamai masu girma a cikin Gwamnatin Jiha. Misali; shin kayi amfani da matsayin kujerarka da kusancin ka da maigirma Gwamna, domin munsan Gwamna yana da kunnen sauraron Jama’a, wajen samawa mutanen mu muƙamai masu tsoka Kamar kujerun Kwamishina, MD-MD, ES ko DGs, da sauran muhimman muƙamai daga wannan yankin namu? Duba da cewa Jagorinmu da Shugabannin mu gogaggu ne, kuma sunanan kara zube. Ko dai zargin da akeyi cewa bakason wani ɗan yankin mu ya samu shiga ƙunshin Gwamnati Kano don gudun kar ya fito neman kujerar Sanata da kai gaskiya ne?
Ko da yake ba na son na tsawaita wannan rubutun a karo na farko, domin ina neman gamsassun amsoshi ne game da tambayoyi na, zan so nayi amfani da wannan dama na tunasar dakai waɗannan buƙatu na jama’a, da kuma nusar dakai cewar ita wannan kujera taka an baka ne domin ka fito daga Kano ta Kudu da kuma wannan yankin namu na Ƙiru/Bebeji.
Wassalam sai ka sake jina a karo na biyu nan ba da jimawa ba.
Shuaibu Haruna
Kiru/Bebeji Social media