Bincike: Shin Sabon Hakimi ya shiga gidan sarautar Bichi kuwa ?

Date:

Daga Abubakar Bichi

 

A jiya litinin rahotannin su ka tabbatar da cewa Hakimin da Sarkin Kano na 16 Khalifa Muhammad Sanusi II ya nada ya shiga garin Bichi domin fara aikin da aka dora masa.

Sai dai wani bincike da jaridar Kadaura24 ta gudanar ya nuna cewa tabbas Wanban Kano, Alhaji Munnir Sanusi Bayero ya shiga karamar hukumar ta Bichi a matsayin Hakimi, kuma ya gana da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar a Islamic Center.

” An gayyato Dagatai da masu unguwanni, inda su ka hadu a Islamic Center ta karamar hukumar Bichi kuma Sabon Hakimi ya yi musu jawabi , daga nan aka ta shi daga taron, kuma shi Hakimin Kano ya koma bai ma nufi gidan sarautar Bichi ba”. A cewar wani shaidar gani da ido

InShot 20250309 102403344
Talla

Kuma binciken ya nuna cewa Hakimin bai shiga cikin gidan sarautar Bichi ba, kuma hasalima da aka kammala taron daga Islamic Center cikin garin Kano ya dawo.

Tun da farko dai lokacin da Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi II, ya naɗa shi Wamban Kano a matsayin Hakimi ya so ya raka shi zuwa Bichi, sai dai kuma a ranar jami’an tsaro su ka yi wa fadar Kano ƙawanya suka hana Sarkin fita domin raka sabon hakimin.

Kano: Hakimin Bichi da Sarki Sanusi II ya nada ya kama aiki

A wani yanayi na bazata Sarkin wanda Magajin Garin Kano Alhaji Nasir Inuwa Wada, ya wakilta ya raka Alhaji Munir Sunusi, zuwa Bichin domin kama aiki a matsayin hakimin Bichi.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai gidan sarautar Bichi a rufe yake, inda jami’an tsaro suke gadin gidan domin hana kowa shiga, sakamakon wani umarni da wata kotu ta bayar na hana kowa shiga gidan har sai an gama dambarar sarautar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...