Daga Sani Idris maiwaya
Karamar Hukumar Dala ta kaddamar da rabon tallafin Shinkafa buhu 1200 Mai nauyin 25kg Wanda Gwamnan Kano ya ke Rabawa a Kananan hukumomi 44 Dake jihar
Da yake Jawabi yayin Kaddamar da rabon Shugaban Karamar Hukumar Dala Alhaji Surajo Ibrahim Imam yabce sun raba shinkafar ne ga Mazabu 12 dake Karamar Hukumar Dala.

Yana Mai cewar Wakilan akwatuna da ma’aikatan Karamar Hukuma da Kuma Jami’an tsaro da Kuma option A and B na Karamar Hukuma harma da kungiyoyin direbobi Nada ga cikin wadanda suka Amfana da tallafin
Alhaji Surajo Ibrahim Imam ya Kuma ce suna Fatan Samun Karin tallafin Shinkafar Duba da irin dubun Al’ummar Dake Karamar Hukumar ta Dala, Sannan ya yabawa Gwamnan Kano Abba kabiri Yusuf bisa Samar da wannan tallafin da yayi a lokacin daya dace.
Bincike: Shin Sabon Hakimi ya shiga gidan sarautar Bichi kuwa ?
Cikin wata Sanarwa da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Karamar Hukumar Dala ta fitar Hassana Aminu tace
Shima a nasa Bangaren a madadin wadan da suka Amfana da tallafin Alhaji Uwaisu Maiturare yayi godiya Ga Gwamnatin Kano da Shugaban Karamar Hukumar Dala Kan Kula da Al’ummar Su a kowani lokaci
Taron rabon tallafin ya samu halartar Shugaban jam’iyyar NNPP na Karamar Hukumar Dala Alhaji Dayyabu Maiturare da Sauran Masu ruwa da tsaki na Karamar Hukumar Dala