Yanzu-yanzu: Tinubu ya aiyana dokar ta baci a jihar Rivers

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya aiyana dokar ta baci a jihar Rivers.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito ana ta rikicin Shugabanci a jihar Rivers, yayin da ake samu rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar da bangaren majalisar dokokin jihar.

InShot 20250309 102403344
Talla

Shugaban kasar ya aiyana dokar ne bayan wata ganawa da yayi da shugabannin hukumomin tsaron kasar kan rikicin jihar ta Rivers.

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Yanzu haka dai za a iya cewa ba gwamnati a jihar har sai matakin da shugaban kasar ya dauka .

Rahotannin sun tabbatar da cewa shugaban kasar ya dakatar da gwamnatin jihar da dukkanin yan majalisar dokokin jihar har na tsahon watanni shida.

Shugaban kasar ya kuma nada  Vice Admiral Ibok Ete Ibas a matsayin mai rikon mukamin gwamnan Rivers State.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...