Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin Tarayya bisa gyarawa da buɗe cibiyar bunƙasa masana’antu da fasahar sadarwa a jihar Kano.

Idan ba a manta ba, a watan Agustan shekarar da ta gabata ne wasu wadanda aka bayyana a matsayin marasa kishin ƙasa suka kai hari, tare da lalata cibiyar ta NCC DIGITAL PARK,wadda take a sakatariyar Audu bako tare kuma da wawashe kayayyakin da aka sanya, a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa.

InShot 20250309 102512486
Talla

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya mika godiyarsa a madadin gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, yayin bikin kaddamar da cibiyar bunƙasa Masana’antu da Fasahar sadarwa wanda Ya gudana a ranar Laraba, Ƙarkashin jagorancin ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki, Dr. Bosun Tijjani.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Mataimakin Gwamnan ya yabawa Ministan bisa cika alkawarin da ya dauka na gyara ginin a yayin ziyarar da ya kawo Kano A kasa da watanni 12 .

An yi gangamin yaki da fadan daba, kwacen waya da shaye-shaye Unguwar Tudun wada

Ya bayyana bude wannan muhimmiyar cibiya a matsayin wadda za ta bunƙasa kwazon matasa da kuma bayar da gudunmmawa ga ci gaban jihar Kano.

A nasa jawabin, Ministan Sadarwa Dokta Bosun Tijjani ya tuno da ziyarar da ya kawo a lokacin da Aka lalata cibiyar , inda ya ce tun lokacin ya lashi takobin tabbatar da an dawo da ita domin cin Moriyar matasan Arewacin kasar Nan.

Ya ƙara da cewa, a daya daga cikin shirye-shiryen da ma’aikatar ta kaddamar a baya-bayan nan, wanda Aƙalla mutane miliyan daya da dubu ɗari takwas suka nema a fadin kasar nan, jihar Kano kadai ta dauki kaso goma 10% na Masu Neman, Wanda hakan wata alama ce da ke nuni bisa yadda Al’ummar jihar ke da alaka da fasahar ƙere-ƙere.

Dakta Tijjani ya kuma yi amfani da damar wajen mika ta’aziyya ga al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar dattijo Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

A Ƙarshe Gwamnatin Jihar Kano Ta naɗa ministan a matsayin Sarkin yaƙin ƙirƙirar fasahar sadarwa, Inda Aka Sanya masa Malafa tare da rataya masa takobi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...