Daga Sani Idris maiwaya
An bayyana Samar da ingantacen labarai a matsayin wata hanya daka iya Samar da cigaba a cikin al’umma
Mai Magana da yawun Gwamnatin jihar Kano Sunusi bature Dawakin Tofa shi ne ya bayyana hakan yayin da ziyaci ofishin yan Jaridu na Fadar Sarkin Kano na 16.

Sunusi bature Dawakin Tofa ya yabawa Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sunusi bisa yadda ya inganta ofishin yan jaridun da ke masarautar Kano tare da Samar da kayan aiki na zamani.
Ta tabbata: NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria
Shi ma a nasa Jawabin Shugaban kungiyar Yan Jaridun na Fadar Sarkin Kano Saddam Nasir Na’ando ya godewa mai magana da yawun gwamnan Kanon bisa wannan Ziyarar daya Kawo
Haka Kuma Saddam Nasir ya baiwa Mai Magana da yawun Gwamnan tabbacin Futar da Sahihan Labarai dan Amfanar Al’umma.
A karshe Shugaban kungiyar Yan Jaridun na Fadar Sarkin Kano ya yabawa gwamnati Kano Kan hadin kan data ke baiwa masarautar Kano a kowani kokaci