Daga Rahama Umar Kwaru
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na tarayyar Nigerian bayan da aka tantance shi.
Nadin nasa, wanda aka amince da shi a yau, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da wanda yake kan mukamin Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Boyo Onanuga ya sanyawa hannu.

An fara bayyana Ogunjimi mai shekaru 57 a matsayin magajin Madehin a watan Disambar da ya gabata.
Ta tabbata: NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria
Sanarwar ta ce sai da shugaba Tinubu ya sa aka bi matakai domin tantance Ogunjimi mai shekaru 57 domin tabbatar da kwarewarsa .
Ogunjimi ya kammala karatunsa na digirin farko a Jami’ar Najeriya, Nsukka, a shekarar 1990, inda ya karanci harkar akanta, sannan kuma ya sami digiri na biyu a fannin Accounting and Finance a Jami’ar Legas.
Mamba ne a Cibiyar Akantoci ta Najeriya
Shugaba Tinubu ya taya Ogunjimi murna bisa nadin da aka yi masa, ya kuma bukace shi da ya dage domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na yi wa Nijeriya hidima cikin gaskiya, kwarewa, da sadaukarwa ga hidimar Nijeriya.