Hukumar hana cin hanci ta Kano ta kama wani Hadimin Gwamnan Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama tare da tsare Daraktan kula da Ma’aikata, da Ma’ajin Kudi na Karamar Hukumar Nasarawa da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Mustapha Maifada bisa zargin karkatar da Naira Miliyan 105.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa an umarce su da su baiwa Mustapha Maifada Naira Dubu 105 don gabatar da wani shiri, a maimakon haka sai suka bashi Naira Miliyan 105.

Sai dai sun ce sun baiwa maifada kudin ne bisa kuskure ntun a watan Nuwambar 2024.

InShot 20250115 195118875
Talla

An bayyana Mustapha Maifada ya fara kashe kudin da aka tura masa inda aka ce ya sayi kadarori da suka haɗa da gidaje sannan ya canja mota shi da matarsa don holewa.

Hukumar karkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado na ci gaba da tsare su don tsaurara bincike.

Ku yi adawa mai ma’ana cikin mutunci da girmamawa – Waiya ga yan adawa

Don jin karin bayani majiyar Kadaura24 ta tuntubi shugaban hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhuyi Magaji Rimingado, amma bai daga wayar da aka buga masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...