Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai martaba Sarkin Rano, Ambasada Dr. Muhammad Isa Umaru, ya bayar da umarnin dakatar da yin duk wani abu na ibada a wata coci da ke cikin garin Rano, bayan da jama’a suka shigar da korafi .
Sarkin ya yanke hukuncin ne bayan da aka gabatar masa da sakamakon binciken kwamitin da aka dorawa alhakin kula da harkokin masarautar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran shiyyar Rano Rabi’u Khalid kura ya aikowa Kadaura24.

Kwamitin wanda aka kafa gabanin tafiyar Sarkin zuwa Saudiyya don gudanar da Ibadar Umara, ya ba da rahoton samun koke daga mazauna yankin dangane da wata majami’a da mabiya addinin kirista ke harkokin bautarsu a wani ginin da ke unguwar Yadi Quarters a cikin garin Rano, ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba.
A wani jawabi da sakataren kwamitin riko Alh.Umar Isa Sarki Said ya gabatar, ya bayyana cewa al’ummar yankin sun nuna damuwa tare da kokawa kan yadda ake gudanar da ayyukan coci ba tare da izini ba.
Hukumar hana cin hanci ta Kano ta kama wani Hadimin Gwamnan Kano
Da samun rahoton kwamitin, Sarkin ya ba da umarnin cewa cocin ta dakatar da ayyukanta cikin gaggawa, yana mai gargadin cewa rashin bin wannan doka na iya haifar da wani sakamako a karkashin ikon masarautar.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa akwai majami’u kusan 27 da ke aiki a sassa daban-daban na karamar hukumar Rano.
Duk Kokarin jin ta bakin shugaban kungiyar kiristoci ta karamar hukumar Rano domin jin karin bayani ya ci tura.