Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Shugaban karamar hukumar garun mallam Aminu Salisu kadawa ya dauki nauyin shirin wayar da kan dalibai Mata na Makarantun sekandire da suke fadin karamar hukumar game da kula da tsaftar jikinsu musamman a lokutan al’ada da yadda za su yi amfanin audugar mata domin kariya daga cututtuka masu hadari yayin al’ada .
Aminu Salisu kadawa ne ya bayyana lokacin da kungiyar Garun Mallam Youth awareness Forum suka ziyarce shi a ofishinsa.
![InShot_20250115_195118875 InShot 20250115 195118875](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2025/01/InShot_20250115_195118875-300x298.png)
Ya ce za a rabawa dalibai mata audugar mata guda dari biyar kyauta, inda kowacce makarantar sakandire ta mata da ta shiga cikin shirin za’a baiwa dalibai 50 audugar cikin mazabu goma da suke a fadin Karamar hukumar garun mallam.
Inganta Noma: Sanata Barau zai tallafawa Matasa 558 daga Arewa maso yammacin Nigeria
Wanna Shiri za a gabatar dashi karkashin kungiyar wayar dakan matasa ta karamar hukumar garun mallam YOUTH AWARENESS FORUM Wanda tuni wanna Shiri ya kankama domin mai girma chairman ya bayar da wanna kudi da za a gabatar da wanna Shiri naira Dubu dari takwas (800,000) a jiya laraba.
Kuma wanna kungiya za ta yi amfani da wakilanta na mazabu domin zakulo Makarantun da zasu amfana da wanna muhimmin program.