Zargin cin zarafi: Ƴansanda sun kama hadimin Gwamnan Kano

Date:

 

Ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ƴansanda, shiyya ta 1 a Jihar Kano ya kama Abba Zizu, Babban Mai kawo Rahoto na Musamman, SSR, ga Gwamna Abba Yusuf wanda ke aiki da Kwamishinan Noma da Albarkatun Kasa, bisa zargin cin zarafin wani ma’aikacin ma’aikatar.

A bayanan da DAILY NIGERIAN ta jiyo an kama Zizu ne bayan da lauyoyin wanda aka ci zarafin, Mahbub Hassan, mai muƙamin Mataimakin Babban Jami’in Noma a ma’aikatar, suka shigar da koke ga AIG.

 

Takardar koken, wacce aka sanya wa hannu ranar 24 ga Janairu, an rubuta ta ne daga Hussain A. Maqari sannan an aika kwafin ta ga kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) reshen Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

A cikin koken, Maqari ya bayyana cewa SSR din ya mari wanda ya ke karewa “sau da yawa” saboda ya bari wani bako ya shiga wurin Kwamishina ba tare da bin ka’ida ba.

A cewar Maqari, sai da Abba Zizu ya kori bakon daga ma’aikatar kafin ya ci zarafin Hassan, inda ya ce ya mare shi sau da yawa bayan ya ci kwalar sa.

Da ya ke zantawa da wakilin DAILY NIGERIAN ta wayar tarho a Kano a ranar Talata, Maqari ya tabbatar da cafke Zizu, amma ya ce an bada belin sa.

Jami’an tsaro sun gano kaburbura 30 a wani Otel

A cewar lauyan, ofishin AIG din, bayan ya saki Zizu l, ya kuka gayyace shi da sauran waɗanda rikicin ya shafa a jiya Talata domin karin bayani da daukar matakan da su ka dace.

“Yanzu da na ke magana da kai, an saki SSR din akan beli. Amma an bukaci mu koma domin ci gaba da bincike da daukar mataki na gaba.

“Ko a Zone 1 din ma sai da ya amsa lefin sa. Ya kuma nuna nadamar hakan,” in ji Maqari.

Da wakilin mu ya tuntuɓe shi, Zizu ya ce “ba haka ba ne ba fa”, inda daga nan bai sake cewa komai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...