Jigin saman Max Air ƙirar Boeing 737 wanda ya dauko fasinjoji daga Lagos zuwa Kano ya tunkuyi ƙasa wajen sauƙa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano a daren Talatan nan.
Wasu Ganau sun shaidawa majiyar Kadaura24 ta Daily Nigerian cewa dirar jirgin ke da wuya tayar gaba ta fashe, kuma ta kama da wuta. Daga nan sai jirjin ya yi taga-taga, goshinsa ya tunkuyi ƙasa.

Tuni dai ma’aikatan kwana-kwana su ka daƙile faruwar gobara a jirgin, kuma fasinjoji su ka yi maza su ka fito daga jirgin.
Gwamnan Kano ya nada mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai
Rahonanni sun nuna cewa babu asarar rayuka ko rauni ga fasinjoji da ma’aikatan jirgin.