Jami’an tsaro sun gano ‘kaburbura’ 30 a wani Otel

Date:

Jami’an tsaro a jihar Anambra sun gano “kaburbura sama da 30 ” a wani otel da ke Oba, karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa rahotanni sun baiyana cewa jami’an tsaro sun gano kaburburan ne a karshen mako bayan samun rahoto daga wani mazaunin yankin.

Ginin, wanda ke kan hanyar Onitsha-Owerri, an yi masa rijista da suna Udoka Golden Point Hotel and Suites, amma ya fi shahara da suna La Cruise Hotel.

InShot 20250115 195118875
Talla

Wani sakon da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar Anambra a X ya ce “otel din yana da kaburbura sama da 30, a bene na karshe tare da wuri na bauta”.

Gwamnan Kano ya nada mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai

Onyeka Ibezim, mataimakin gwamna a jihar Anambra, ya jagoranci jami’an tsaro wajen rusa ginin a ranar Asabar.

Da ya ke magana da ƴan jarida bayan sintirin, Ibezim ya ce babu gurbi ga aikata laifi a wannan jihar ta kudu maso gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...