Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ba da tabbacin ɗaukar matakin daya dace akan duk kwamishinan da ya yi wasa da aikin da gwamnati ta dora masa.
” A wannan lokaci da muke ciki ba za mu lamunci dukkan wani sakaci daga wani kwamishina ba, dan haka dukkan kwamishinan da ya kawo wasa za mu ɗauki matakin da ya kamata akan shi” .
Kadaura24 ta rawaito Alhaji Abba Kabir ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar zartarwa karo na 23 da aka gudanar a gidan gwamnati.
Gwamna Yusuf ya kuma ja hankalin sababbin kwamishinoni da ya nada da su haɗa kai da sauran kwamishinoni dare da aiki guri guda domin ciyar da jihar Kano gaba
Yayin zaman majalisar zartarwar gwamna Abba Kabir ya kuma bayyana wasu shirye-shiryen da gwamnatinsa za ta gabatar nan bada jimawa ba.