Mun daidaita tsakaninmu ni da Alpha – G-Fresh

Date:

 

Shahararren jarumin Tiktok G-Fresh Al-amin, ya bayyana cewa yanzu sun dawo jituwa da sabuwar masoyiyarsa, Alpha Charles Borno, bayan rashin fahimta da suka samu.

A bidiyon da suka wallafa a shafinsu na sada zumunta, suna rungume da juna, G-Fresh, ya nemi afuwar masoyansu kan maganganun da ya yi a baya.

Ya nemi afuwar waɗanda suka ɓata musu rai, tare da sanar da su cewa an sanya ranar bikinsu a ranar Asabar.

Talla

A ranar Talata, G-Fresh ya fito a bidiyo, inda ya nuna cewa lamarin aurensu da Alpha yana cikin matsala, kuma akwai yiwuwar a dakatar da shi.

Wannan ya haifar da muhawara a soshiyal midiya, inda wasu ke ganin cewa ba auren da za su yi ba, sai dai neman hankalin jama’a.

Sai dai a ranar Laraba, G-Fresh, ya kawo ƙarshen wannan magana, inda ya bayyana cewa yanzu komai ya dawo daidai.

Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

“Mun samu daidaito tsakanina ni da amaryata. A baya an samu wata tangarda, amma yanzu komai ya gyaru.

“Don haka, duk wanda muka ɓata masa rai, muna neman afuwa. In sha Allah, bikin zai kasance tsakanin sati huɗu zuwa wata ɗaya.

Zamu sanar da lokacin. Yanzu Alhamdulillah! Ina cikin farin ciki,” in ji G-Fresh.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...