Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi martani game da kalaman jagororin Jam’iyyar APC da suke cewa za su kwace Kano a zaben 2027.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, ya ce gwamnan ya bayyana hakan yayin taron baiwa mata jari na wata-wata da aka gudanar jiya a dakin taro na Coronation.
Gwamnan ya jaddada cewa bai damu da zaben 2027 ba, domin yasan kuwa Allah ne yake bayar da mulki ba wani ba.
“Abun da ya ke gabana shi ne na sauke nauyin da al’ummar jihar Kano suka dora mi a zangon farko na gwamnatina, Ina son mutanen Kano su yi mani hukunci da aiyukana ,” in ji Gwamnan
Gwamnan ya koka da yadda makiya Kano da ke fakewa da adawa suke kokarin haifar da rikicin siyasa a jihar.
Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi
“Mun kayar da ku a zaben 2019 da 2023. Mun yi nasara a kansu a lokacin da ba mu da wani mukami na siyasa—ko da kuwa kansila. Amma Allah Ya sa mu ka samu nasara da gagarumin rinjaye,” inji shi.
Gwamna Yusuf ya kuma gargadi shugabannin jam’iyyar APC na Kano da su guji furta kalama da zasu iya tayar da hankali da kalaman tsoratarwa ga al’umma, su bari lokaci yayi masu zabe su yanke hukunci.
“An rubuta a kaddara cewa zan zama Gwamna, kuma Imanina ne da sallamawa ga yardar Allah ta sa Allah ya bani, to don me yanzu zan daga hankali na sai na sake yin Zango na biyu?” Gwamnan ya tambaya.