Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yabawa shugaban kungiyar NNPP Kwankwasiyya Media Forum ta jihar Kano Alhaji Nura Bakwankwashe saboda irin gudunmawar da yake baiwa gwamnatinsa ta fuskar yada labarai.
” Nura Bakwankwashe mutam ne mai hakuri da karbar kaddara mai kyau ko akasin ta , shi yasa muke kaunarsa saboda kishin da yake da shi ga jihar Kano da al’ummarta”.
Gwamnan Kano ya yabawa Nura Bakwankwashe ne yayin wani taron ba da tallafi da gwamnatin jihar Kano ta baiwa masu magana a kafafen yada labarai a gidan gwamnatin Kano.

Kungiyar NNPP Kwankwasiyya Media Forum ce dai ta shirya taron domin tallafawa ya’yanta da ma wasu daga cikin yan Jam’iyyar adawa ta APC domin raje musu radadi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma yaba da yadda Nura Bakwankwashe yake kishin ganin an taimakawa ya’yan kungiyarsun da al’ummar jihar Kano.
Da dumi-dumi: Kwamishina a Gwamnatin Kano ya ajiye aiki
” Gaskiya da rikon amana da kishin Nura Bakwankwashe shi ne abun da ya kawo mu wannan waje, ina so ku sani son wannan tafiya da kishin jihar Kano ne yasa Nura Bakwankwashe yake tare da mu ba mukami ko wani abun duniya ba”. Inji Gwamna Abba Kabir Yusu
Ya yabawa dukkanin masu kare manufofin gwamnatin jihar Kano a kafafen yada labarai saboda yadda a koda yaushe suke fadi tashi don kare muhibbar gwamnatin a idon duniya.
Kungiyar Shugabannin masu rinjaye (Majority Leaders) ta Kano ta zabi Sabbin Shugabanninta
“Wannan tallafin mun baku ne a matsayin somin tabi, kuma ba biyanku muka yi ba kawai kyautatawa ce da kuma nuna godiya akan aiyukan da kuke yiwa mana, haka kuma ina baku tabbacin nan gaba wasu abubuwan alkhairi na nan tafi a gare ku da yardar Allah”. Inji Gwamna Yusuf
Kimanin sama da Naira Miliyan 30 Gwamnatin jihar Kano ta rabawa ya’yan kungiyar NNPP Kwankwasiyya Media Forum dake karkashin jagoranci Nura Bakwankwashe da Alhajiji Nagoda da Samaila Murtala Zawa’i.