Kungiyar Shugabannin masu rinjaye (Majority Leaders) ta Kano ta zabi Sabbin Shugabanninta

Date:

Daga Nura Adam Lajawa

 

Kungiya Shugabannin masu rinjaye (Majority Leaders) ta jihar Kano ta zabi
HON. Muttaka Lawan Lajawa Kansilan Mazabar Lajawa kuma Majority Leader na karamar hukumar Wudil a matsayin shugabanta na jiha.

Kungiyar dai ta kunshe duke wani kansila da yake da mukamin shugaban masu rinjaye na majalisar karamar hukumarsa a fadin jihar Kano.

An dai gudanar da zaben ne jiya lahadi a birni Kano.

Jim kadan da zabarsa a matsayin shugaban kungiyar Shugabannin masu rinjaye na jihar Kano Hon. Muttaka Lawan Lajawa ya sha alwashin yada kawunan yayan kungiyar.

Talla

” Wannan mukamin Allah ne ya bani shi kuma ina neman taimakonsa kan wannan jagoranci da ya bani, ya bani damar kawo cigaban da za’a dade ana alfahari da ni”. Inji Hon. Muttaka Lajawa

Ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun rika tattaunawa a tsakanisu domin ganin sun kawo abubuwan da za su ciyar da jihar Kano gaba.

Ina mika Sakon godiya ga duk ya’yan wannan kungiya da har suka zabe ni suka bani damar jagorantarsu, ina basu tabbacin yin adalci daidai gwargwado. Haka ma ina mika Sakon godiya ga Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da jagoranmu sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa gudunmawar da suka bayar har aka gudanar da zaben lafiya ba tare da wata matsala ba.

Ga Jerin Sunayen Shugabannin kungiyar Shugabannin masu rinjaye (Majority Leaders) na Jihar Kano:

Da dumi-dumi: Kwamishina a Gwamnatin Kano ya ajiye aiki

1. Hon. Muttaka Lawan Lajawa (Wudil) Chairman

2. Hamisu Idris Amuma (Bichi) – V/Chairman

3. Ibrahim Garba Dan waire (Dala) Secretary

4. Haruna Uba Aliyu (Sumaila) Ass. Secretary

5. Musbahu Galadima ( Kabo) Org/ Secretary

6. Basiru Ali Tanko (Rogo) (Treasure

7. Hassan Sagir (Kumbotso) P R O

8. Abba Adam Nadabo (Gabasawa) F/ Secretary

9. Kabiru M Ya’u (Bebeji) Auditor

10. Mukhtar Ya’u Sani (Tarauni) Welfare

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade, tare da sanya ranar rantsar da sabbin kwamishinoni

Kano South

11. Sa’idu Hassan (Kiru) Zonal Chairman

12. Shu’aibu Abdulmumini ( Ajingi) Zonal Sec.

13. Auwal Sa’ad ( Kibiya) Zonal P R O

Kano Central

14. Sani Halilu (Gezawa) Zonal Chairman

15. Ashiru Garba (Gwale) Zonal Sec.

16. Abdulkadir Aliyu Sani ( G/Malam) Zonal P R O

Kano North

17. Yusuf Husaini Muhd (Ghari)Zonal Chairman

18. Aliyu Umar Ibrahim ( Gwarzo) Zonal Sec.

19. Mutawakil Harun (D/Tofa) Zonal P R O

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...