Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da ajiye aiki da Engr. Muhammad Diggol, yayi a matsayinsa na kwamishinan ma’aikatar bibiyar aiyuka nan take.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24 a ranar Lahadi.

Tun a farkon mulkinsa gwama Abba Kabir Yusuf ya nada Engr. Muhammad Diggol a matsayin kwamishinan sufuri, kafin daga bisani ya saura masa wajen aiki zuwa ma’aikatar bibiyar aiyuka inda a nan ne yayi murabus .
Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa ga Engr. Diggol bisa kokarinsa da jajircewarsa, sadaukarwa, da kuma bin ka’idojin aiki a lokacin da yake zama dan majalisar zartarwa ta jiha.
Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade, tare da sanya ranar rantsar da sabbin kwamishinoni
A cewar sanarwar, Gwamnan ya yiwa Engr. Doggol fatan alheri a harkokin da zai sanya a gaba.
Sanarwar dai ba ta bayyana dalilin da ya sanya kwamishinan ya ajiye aikinsa ba.