Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, Ya Taya Gwamna Yusuf Murnar Cika Shekaru 62, Ya Bayyana Shi A Matsayin Shugaba Mai Hange

Date:

Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice dake Kano Auwal Lawal Muhammad ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa da himma wajen yiwa al’umma hidima.

A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, Alh Auwal ya ce, “Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu dama da lokaci na shaida zagayowar ranar haihuwar ka.

Ya yaba da nasarorin da gwamnan ya samu a fannin ilimi, kiwon lafiya, da samar da ababen more rayuwa, yana mai cewa hakan na nuni da irin kishi da jajircewarsa wajan ci gaban jihar Kano.

Talla

Lawal ya yaba wa kokarin da gwamnan ya kawo cikin kankanen lokaci, inda ya ce hakan sun zama abin koyi ga sauran gwamnoni, kuma ya bar tarihi da zaba jima ana tunawa dashi.

Ya kuma nuna jin dadinsa kan yadda Kano ke sauyawa cikin gaggawa karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida). Salon shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf a cewar Lawal ya kawo sauyi mai kyau ga jihar Kano.

Acewar Lawan “Yunkurinsa na tabbatar da gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari ya sa jama’a ke girmama shi da kuma yaba masa kan ayyukan dayake aiwatarwa.

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade, tare da sanya ranar rantsar da sabbin kwamishinoni

Shugaban Asibitin ya kuma yaba kan kokarin da gwamnan keyi na inganta fannin kiwon lafiya, inda ya bada misali da yadda Gwamnan ke gyarawa da inganta asibitoci, samar da kayan aikin likitanci na zamani, da horar da ma’aikatan lafiya.

Ya kuma yaba da ayyukan da gwamnan ya yi a fannin ilimi da suka hada da gina sabbin makarantu, gyara wadanda ake da su, da kuma samar da kayayyakin ilimi.

Daga bisa kwamaret Auwal Lawan ya yaba wa gwamnan bisa sadaukarwa da tsantsar tausayi da yake nunawa, wadanda hakan ke tasiri a rayuwarsu.

Yayin da Gwamna Injiya Abba Kabir Yusuf ke murnar cika shekaru 62 a duniya, Lawal ya yi addu’ar Allah ya kara masa lafiya da basira da kuma kwarin gwiwa na ci gaba da yi wa al’ummar jihar Kano hidima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...