Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nade-naden mukamai da dama da nufin karfafa gwamnatinsa don gudanar da shugabanci nagari.
Hakan kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.
Wadanda aka nada din sune kamar haka:

1. Hon. Ahmad Muhammad Speaker: a matsayin mai ba shi shawara na musamman akan harkokin yada labarai.
2. Engr. Ahmad a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan Ayyuka.
3. Malam Sani Abdullahi Tofa: mai ba gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman.
4. Hon. Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin shugaban hukumar kula da kananan hukumomin Kano .
5. Hajiya Ladidi Ibrahim Garko a matsayin shugabar hukumar ma’aikatan ta jihar Kano.
Wadanann mutanen biyu da aka nada suna cikin tsoffin kwamishinonin da aka cire su kwanan nan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa Gwamnan ya shirya bikin rantsar da su a ranar Litinin 6 ga watan Janairun 2025 da karfe 11:00 na safe a zauren taro na fadar gwamnatin Kano.
Za kuma a hada rantsuwar ta su da ta kwamishinoni bakwai da majalisar dokokin jihar Kano ta tantance kwanan nan, da kuma dukkan sabbin mashawarta na musamman da aka nada.
Sanarwa ta ce wadannan nade-nade sun fara aiki ne nan take.