Ƙungiyar agaji ta likitoci Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce a cikin watanni takwas ɗin farko na wanan shekarar ta bayar da magani ga ƙananan yara 52,725 masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki a arewacin Najeriya.
Shugaban MSF, Dr Christos Christou, ya shaida wa manema labarai a Abuja a ƙarshen mako cewa adadin yara masu fama da ƙarancin abinci mai gina jikin ya ninka a arewacin Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce daga watan Janairu zuwa Agusta, MSF ta tattara alkaluma da ke cewa an samu ƙarin ƙananan yara da ake kwantarwa asibiti saboda da kashi 51 cikin 100.
APC ta tsayar da Aliyu Harazimi Rano takarar shugaban karamar hukumar Rano
”Ana cikin haka kuma sauran cutuka masu kama ƙananan yara sun samu damar shiga jikin yara da dama a Najeriya.,” in ji shi.
Dr Christou ya ƙara da cewa sun yi maganin sauran cutuka ga ƙananan yara 12,500 bayan waɗanda ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki, lamarin da ke nuna cewa yawansu ya ruɓanya wanda aka samu a bara.