Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da wasan kwaikwayo ta jihar Kano (RATTAWU), Comrade Babangida Mamuda Biyamusu, ya mika sakonsa na taya murna ga sabon zababben shugaban kungiyar na kasa, Prince Emeka Kalu, tare da saura wadanda za su jagoranci kungiyar wanda aka gudanar a jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Comrade Babangida Biyamusu ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Ya yi fatan sabbin Shugabannin kungiyar za su yi aikin sosai don samar da cigaba ga kungiyar da kuma ya’yan kungiyar.

A yayin zaben, Prince Emeka Kalu ya samu nasarar zama shugaban kungiyar na kasa da jimillar kuri’u 276, sai Misis Opi Erik da ta sami kuri’u 141, Dare Duresemi kuma ya samu kuri’u 126, Jespa kuma ya samu kuri’u 5.
An kuma zabi Kwamared Babangida Umar Zurmi mataimakin shugaban kungiyar na kasa.
Sauran mataimakan shugabannin da aka zaba sun hada da:
– Murtala Usman Madobi (North West, Jigawa State)
– Ahmed Muhd (Ma’ajin Kasa)
– Nwanwevele Azvewa (Kudu maso Gabas)
– Dahiru Aliyu Dadi (North East)
– Komolafe Felix Olukole (Kudu maso Yamma)
– Terry Isaac Idahor (Kudu ta Kudu)
– Umar Abdullahi Kinta (Arewa Ta Tsakiya).
Sauran wadanda aka zaba sun hadar :
– Izang Francis Atsen – Sakataren Yada Labarai
Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya
– Enegide Charles – Sakataren kudi
– Fatima Galadima – National Auditor
– Joseph Olujimi Gansallo
Shugaban kwamitin zaben Kwamared Abubakar Musa Dakina ya yiwa sabbin Shugabannin fatan samun nasara a jagorancin da za su yiwa kungiyar RATTAWU ta Kasa.