Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugabar kungiyar yan jaridu mata NAWOJ a reshen jihar Kwamared Bahijja Malam Kabara ta bukaci al’ummar musulmin kasar nan da su yi koyi da kyawawan dabi’un manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama .
Kwamared Bahijja Kabara ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar kungiyar Maryam Muhammad Yakasai ta sanyawa hannu kuma ta turowa Kadaura24.
Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta baiwa Sarki Aminu sabon Umarni
Ta yi kira ga matan da su rubanya kokarinsu ta hanyar bin koyarwar Annabi S A W wajen biyayya ga mazajensu da kuma kyautata alaka da makwabta.
Rashin kyawun hanya: Al’ummar Dan Dinshe na bukatar agajin gwamnan Kano
Kwamaret Bahijja ta kuma yi kira ga mata da su koya wa ‘ya’yansu tarihin Annabi Muhd tare da yin koyi da halayensa domin kyautata rayuwar al’umma.
Hakazalika Kwamared Bahijja Kabara ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa marasa galihu kamar yadda aka koya daga koyarwar Annabi Muhd. S.A.W