Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar kano ta sanar da dage dokar hana fita da ta sanya sakamakon yadda zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta rikide zuwa tashin hankali.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa gwamnatin jihar kano ta sanya dokar ne tun a ranar Alhamis ranar farko kenan da fara Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa bayan wasu bata gari sun fake da zanga-zangar su ka rika fasawa da sace kayan gwamnati da na al’umma.
Dan Bello ya sanya wa jam’iyyar APCn Kano sharadin dakatar da yi mata bankade-bankade
Kwamishinan yada labarai na jihar kano Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kano.
Yace gwamnatin ta dauki wannan matakinne sakamakon yadda al’amura suka koma daidai, zaman lafiya ya dawo jihar yadda ya dace.
Hakan dai yana nufi an dage dokar kwata-kwata a kwanaki masu zuwa, mutane za su iya cigaba da harkokinsu na yau da kullum.