Daga Rahama Umar Kwaru
Majalisar dokokin jihar Kano ta fada cikin rudani lokacin da kakakin majalisar Jibril Isma’il Falgore ya kirawo tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa.
kakakin majalisar cewa Ganduje shugaban rikon jam’iyyar APC ne a lokacin da yake mika sakon ta’aziyya ga uwargidansa Farfesa Hafsat Ganduje kan rasuwar mahaifiyarta, wanda ya haifar da zazzafar muhawara.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar Labaran Abdul Madari da wasu ‘yan majalisar APC ne suka fito da batun, inda suka ce yanzu Ganduje ne cikakken shugaban jam’iyyar APC na kasa ba shugaban riko ba ne.
Daga bisani majalisar ta dage zaman har zuwa ranar Talata.
A wannan rana ce dai majalisar dokokin jihar Kanon ta dawo zama tun bayan hutun kwanaki 48 da ta yi, wanda ta tafi bayan zartar da kudirin dokar soke masarautu biyar na jihar Kano.
Samoa: Gwamnatin Tinubu na yunkurin danne hakkin yan jarida – Atiku Abubakar
Rahotanni sun nuna cewa an majalisar ta jinkirta komawa bakin aikinta ne saboda matsalar tsaro da ta taso bayan rushe masarautun.
Nigerian Tranker