Samoa: Gwamnatin Tinubu na yunkurin danne hakkin yan jarida – Atiku Abubakar

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya yiwa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 da ta gabata, Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da yunkurin gwamnatin jam’iyyar APC mai mulkin Nigeria karkashin jagorancin Bola Tinubu, na murkushe yancin yada labarai da kafafen yada labarai ke da shi a cikin kwaskwararren kundin tsarin mulki kasa na 1999.

“Ba karamar barazana ba ce ga tabbatar da dimokaradiyyar Nigeria, wadda ta ke dambare akan durakun bangarori guda hudu na zartarwa, dokoki, Shari’a da na yan jarida wadanda hakkin sanar da al’umma halin da kasa ta ke ciki ya rataya a wutansu”.

Talla

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka aikowa kadaura24.

Abdulmumini Kofa ya jagoranci zaman farko a matsayin shugaban kwamitin gidaje da muhalli

Ya yi kira ga yan jarida a Nigeria da cewa kada su bari wannan barazanar ta tsorata su, ta yadda zasu kasa sanar da al’umma rawar da gwamnatin da ke mulkinsu ke takawa wajen tasarrafi da al’amuran da suka shafi rayuwar su da walwalar su.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnatin tarayyar Nigeria na shan suka tun lokacin da kamfanin jaridar Daily Trust suka rawaito cewa gwamnatin ta sa hannu kan yarjejeniyar Samoa wadda ake zargin cewa akwai batun auren jinsi a cikin ta.

Lamarin da yasa gwamnatin tarayyar ta musanta har ma ya yi barazanar daukar matakin Shari’akan Kamfanin jaridar Daily Trust.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...