Gwamnan Kano ya zargi gwamnatin Ganduje da ɗaukar nauyin harkar daba a jihar

Date:

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin da ta gabace shi da ɗaukar nauyin ‘yan daba a Kano.

Yayin da yake jawabi a gabanin taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar ranar Asabar a fadar gwamnatin jihar, Gwamnan Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan halin taɓarɓarewar tsaro da jihar ke fuskanta, musamman harkar dabanci.

”Kowa ya sani kafin mu shigo gwamnati, waccan gwamnatin da ta shuɗe ita ce ke ɗaukar nauyin ‘yan daba, ita ce ke sa su suna yin abin da duk suka ga dama suna cutar da al’umma”, in ji gwamnan na Kano.

Rikicin Sarautar Kano: Yan Sanda Sun Dauki Bangare – Gwamnan Kano

Gwamnan ya kuma ce a lokacin yaƙin neman zaɓensa ya yi alƙawarin kakkaɓe matsalar daba a Kano.

Ya kuma ce bayan nasararsa a zaɓen gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin daƙile matsalar.

Amma ya ce a cikin wata biyu da suka gabata wasu da ya kira ”maƙiyan jihar” suka maido da harkar daba.

Gwamnatin Kano ta Gargaɗi Al’umma Game da Amfani da Ruwan Sama

Inda ya yi zargin cewa wasu sun ɗauko hayar wasu ‘yan daba daga makwabtan jihohi domin su kawo wa zaman lafiyar jihar cikas.

Abba Kabir ya kuma yi barazanar fara kiran sunayen mutane da yake zargi da ɗaukar nauyin ‘yan daba a jihar.

Haka kuma gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ya ce wasu na zuwa ofishin ‘yansanda domin fito da ‘yan daba idan hukuma ta kama su.

Inda ya yi barazanar cewa duk mutumin da gwamnatinsa ta sake samu da wannan laifi to za a gurfanar da shi a gaban kotu, domin yin bayanin dalilinsa na ɗaukar nauyin ‘yan daba a Kano.

A baya-bayan nan dai jihar Kano na fuskantar faɗace-faɗacen ‘yan daba, waɗanda ke cin karensu babu babbaka a wasu unguwannin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar lantarki

Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya...

Aiyuka 5 da Gwamnan Kano ya yi alkawarin yi, bayan dakatar da rusau a Rimin Zakara

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci garin Rimin Zakara...

Shugaban K/H Garun Mallam zai Raba Audugar Mata 500 ga Makarantun Sakandiren Matan yankin

Daga Safiyanu Dantala Jobawa Shugaban karamar hukumar garun mallam Aminu...

Inganta Noma: Sanata Barau zai tallafawa Matasa 558 daga Arewa maso yammacin Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...