Daga Rahama Umar Kwaru
Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU reshen jami’ar Bayero ta Kano, ta yi watsi da nadin da aka yiwa Dakta Nasiru Gawuna a matsayin shugaban majalisar gudanarwar jami’ar.
Kadaura24 ta rawaito shugaban kungiyar, Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kano.
Ya ce tsarin da aka bi har aka nada ‘yan siyasa a majalisun gudanarwar manyan makarantun ilimi na kasa ya saba wa dokokin da aka samar domin irin wannan nade-naden.
Gwamnan Kano ya zargi gwamnatin Ganduje da ɗaukar nauyin harkar daba a jihar
“Dole ne mu bayyana rashin jin dadinmu akan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na nada manyan ‘yan siyasa a majalisar gudanarwar jami’o’i wanda hakan bai daidai ba”.
Siraj ya jaddada cewa “Sharuɗɗan irin waɗannan nade-naden a bayyane suke, domin suu fifita nada ƙwararrun malamai a Majalisar gudanarwar”.
Rikicin Sarautar Kano: Yan Sanda Sun Dauki Bangare – Gwamnan Kano
Shugaban ya kara da cewa korar tsohuwar majalisar da kundin tsarin mulki ya ba ta wa’adin shekaru 4, bayan sun yi shekara daya a ofis
Don haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da Sanata Udo Udoma shugabancin majalisar gudanarwar kasar domin kammala wa’adinsu domin tabbatar da doka da oda.