Gwamnatin Kano ta Gargaɗi Al’umma Game da Amfani da Ruwan Sama

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

A yayin da yanayin damina ke ci gaba da kankama, gwamnatin jihar kano ta buƙaci al’ummar jihar da su kula sosai wajen amfani da ruwan sama a wajen sha da sauran ayyukan yau da kullum.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi gargaɗin a cikin wata sanarwa da ta fito daga sashin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin, Ibrahim Abdullahi, wadda aka aikowa kadaura24.

Kwamishinan ya ce lokacin saukar ruwan sama lokaci ne da ke tattare da hatsari na samuwar cutar amai da gudawa wanda tuni wasu jihohi a Najeriya sun gamu da matsalar, yana mai cewa wannan dalili ne ya sa wajibi a ja hankalin al’umma da cewa rigakafi ya fi magani.

Karin Haske Kan Hukuncin Kotu Game da Rikicin Sarautar Kano

Dakta Labaran ya ci gaba da cewa wajibi ne mutane su kula da abin da za su ci da wanda za su sha, musamman kayan lambu, kayan marmari da kuma ruwan sha, ya ƙara da cewa tilas jama’a su kula da waɗannan ƙwarai da gaske domin kar a ci ko a sha gurɓataccen abinci ko ruwa.

“Yana da kyau mutane su fahimci cewa, ruwan saman da ake yi a farkon damina ba mai kyau ba ne. Idan ya zama dole sai an yi amfani da shi, to a tabbata an yi amfani da dukkan sinadaran tsaftace ruwa; a dafa a tace kafin a yi amfani da shi. Yin haka zai taimaka sosai wajen hana kamuwa da cutar amai da gudawa”, ya ja hankalin al’umma.

Kwamishinan ya kuma ja hankalin jama’a wajen amfani da kayan lambu da na marmari, inda ya ce wajibi su ma a tabbatar an wanke su sosai da ruwa mai tsafta kafin a yi amfani da su kasancewar sayo su ake yi daga kasuwa ba tare da cikakkiyar tsafta ba.

Gwamnatin Kano ta baiwa yan sanda sabon umarni akan Sarki Aminu Ado Bayero

Daga nan sai ya tabbatar da ƙudirin gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf na ci gaba da kula da lafiyar al’ummar jihar Kano a ko da yaushe, kasancewar fannin lafiya na ɗaya daga ɓangarorin da Gwamnan ya bai wa muhimmanci.

Daga ƙarshe, Dakta Labaran ya ja hankalin al’umma da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen ziyartar asibiti mafi kusa yayin da duk aka kamu da rashin lafiya, yana mai addu’ar Allah Ya kiyaye jihar Kano da al’ummarta, “Amma fa wajibi sai mun kiyaye kanmu, sannan Allah zai kiyaye mu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar lantarki

Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya...

Aiyuka 5 da Gwamnan Kano ya yi alkawarin yi, bayan dakatar da rusau a Rimin Zakara

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci garin Rimin Zakara...

Shugaban K/H Garun Mallam zai Raba Audugar Mata 500 ga Makarantun Sakandiren Matan yankin

Daga Safiyanu Dantala Jobawa Shugaban karamar hukumar garun mallam Aminu...

Inganta Noma: Sanata Barau zai tallafawa Matasa 558 daga Arewa maso yammacin Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...