Yanzu-yanzu: Muhuyi Magaji Ya Sake Kaddamar da Sabbin Zarge-zarge akan Ganduje

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce zata sake gurfanar da wani tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje bisa zargin almundahana da almubazzaranci da dukiyoyin al’umma.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci, Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels Television a ranar Talata.

APCn Kano ta yi Martani Kan dakatar da aka yiwa Ganduje

“Yanzu haka da nake magana da ku, muna kan binciken wasu kudin har kimanin N51.3bn wadanda gwamnatin tarayya ta turowa kananan hukumomi kuma aka dauke su daga asusun gwamnati aka aika wa wasu mutane, kuma mun gano mutanen da aka turawa din.”

Magaji ya yi zargin cewa a watan karshe na gwamnatin Ganduje ta kwashi Naira biliyan 1 daga asusun gwamnati, da sunan za’a yi aikin hanya da su, amma sai muka ga an tura da kudin ga wasu kamfanonin Chanji Kudaden kasashen waje.

Yanzu-Yanzu: APC ta Dakatar da Ganduje Daga Jam’iyyar

“Muna da wata kara da muka shigar akan Naira biliyan 4, wadda aka fitar da ita daga asusun ajiyar kudaden shiga na jihar Kano zuwa wani kamfanin noma. Duk wadannan kararraki suna gaban kotu,” inji shi.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Kano, wanda ya ce ana kallonsa a matsayin “mai taurin kai” saboda harkar halasta kudaden haramun batu ne da gwamnatin tarayya ce da hurumi akai, amma yace hukumarsa na da hakkin bincike akan zargin almundahana da ake yiwa Ganduje .

Magaji yace ya fara binciken gwamnatin Ganduje ne tun yana gwamnan Kano. Ya ce bai kamata a samu shafaffu da mai a yaki da cin hanci da rashawa a jihar ba.

“Abun dadin shi ne kyawun a Najeriya ba Wanda ya Isa yace yafi karfin a gurfanar da shi a gaban Shari’ar don haka kawai Ganduje ya shirya gurfana a gaban kotu domin ya kare kansa.”

Idan za’a iya tunawa kadaura24, gwamnatin jihar kano za ta gurfanar da Ganduje a ranar Laraba 17 ga Afrilu, 2024, bisa tuhumar da ake masa na cin hanci da rashawa, karkatar da kudade, da almubazzaranci da wasu kudade da suka hada da zargin karbar cin hanci da rashawa $413,000 da kuma N1.38bn.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...