APCn Kano ta yi Martani Kan dakatar da aka yiwa Ganduje

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta dau tsauraran matakai kan wasu jiga-jigan jam’iyyar na mazabar Ganduje da suka ce sun dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Umar Abdullahi Ganduje.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito jam’iyyar APC ta mazabar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ta dakatar da Ganduje.

Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Dawakin Tofa, Inusa Dawanau, ya shaida wa manema labarai cewa, wadanda suka dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa abun da suka yi ya sabawa doka, kuma suna zargin yan adawa ne suka kitsa lamarin .

Yanzu-Yanzu: APC ta Dakatar da Ganduje Daga Jam’iyyar

Yace kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na jihar ya ce sun dakatar da wadanda suka ce sun dakatar da Ganduje har na tsahon watanni 6, sannan kuma an kafa kwamitin bincike na musamman domin tabbatar da wasu zarge-zarge da ake yi musu.

Shugaban Jam’iyyar na Kano, Abdullahi Abbas, ya ce sun amince da shawarar da shugabannin Jam’iyyar suka dauka.

Ali Nuhu, Ali Jita, Abale da Wasu Yan Kannywood syun Yiwa Adam A Zango Martani

“Muna da hujjojin da zasu tabbatar da ganawar da wadancan mutane suka yi da jami’an gwamnatin jihar kano. Kwamitin ayyuka na jihar ya amince da sanya musu takunkumi na tsawon watanni shida, kuma yanzu haka sun dakatar da su.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...